Breaking News

Furar Danko Book 2 Page 10

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗


           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟........Ko parking bai gama yi da ƙyau ba Uncle Yousuf ɗin ya fice, ba'a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito ɗauke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya buɗe masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA'S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin.


       Duk wani kai kawo da ake a kanta shi dai nashi ido ne. Yayinda acan ƙasan zuciyarsa yaketa tufƙa da warwara akan abubuwa da dama. Musamman akan abinda ya dawo da shi aiki cikin wannan family ɗin a karo na biyu. Tabbas ya amshi aiki, sai dai kuma bada manufar wanda ya bashi aikin ba. Dan ko kaɗan baiji wani kurari daga gargaɗinsa sun tsoratashi ba. Hasalima shi wanda ya bashi aikin da yasan shi ɗin wanene maybe dabai bashi ɗin ba. Amma zaiyi, dan in bai amsa ba zai bama wani da zai iya masa yanda yake so... Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa tunani, ya ciro wayar daga aljihu yana miƙewa ya fito. Sallama yay bayan yakai wayar kunnensa, daga haka bai sake magana ba sai saurare. Bayan ya katse kiran ya cire wayar a kunnensa yana furzar da iska kaɗan. Cike da iya nazari yake bin farfajiyar asibitin da kallo a kaikaice, can idonsa ya sauka akan abinda yake nema. Basarwa yay ya share na wasu mintuna, kafin ya nufi fita gate ɗin a nutse. Dai-dai inda almajirai ke zaman bara ya dakata, naira ɗari biyu dake aljihunsa ya ciro ya saka a kwanon barar wani gurgun almajiri dake kan katako mai tayu, almajirin ya shiga jera masa addu'a. Yana ƙoƙarin juyawa matashin saurayin dake gefensa kaɗan yazo ta gefensa suka bangaji juna, kallon juna sukai kamar cikin jin haushi. Sai dai shi saurayin yay saurin faɗin, “Yi haƙuri abokina ban lura bane ba”. Kai kawai ya kaɗa masa yabar wajen batare daya tanka ba.

      Maimakon komawa cikin asibitin sai ya samu waje a harabar ya zauna abinsa, can kusan mintuna uku yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu sai yaji takardar da saurayin nan ya saƙala masa a aljihu sanda sukai karo batare da ya lura ba. Zarota yay ya warware cike da mamaki, sai kuma ya shiga ɗan waige-waige amma babu alamar saurayin ko wani da zai ce hankalinsa a kansa yake. 

        _“Ni kamar iska nake, a duk lokacin data kaɗa sai anji sautinta a dukkan ƙofofin gashi na jiki. Idan kuma nai shirin zuwa waje matsayin guguwa tarwatsa komai da kowa na gari nake hatta ruwan kogi baya tsira da ga mamayata. Ka kula, in ba hakaba ni na ƙulleka a cikin ƙullina Aliyu Hydar Mawashi”_.

     Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi na ɓacin rai. A take zuciyarsa ta fara kaikawo da sauri-sauri cikin ƙirjinsa. Takardar ya ninke ya maida aljihu, yana batun tashi waya ta sake yin ringing a jikinsa. Wayar dai da Alhaji nan ne ya bashi jiya, yana kuma ƙyautata zaton takardar nan ma da ga garesa take duk da ya kirashi ne ɗazun a wayarsa. Shi sam yama manta da wayar. Cirota yayi daga aljihun, kamar bazai ɗaga ba sai kuma miya tuna ya ɗaga tana gab da tsinkewa ya kai kunne. Baiyi magana ba daga can ma akai shiru, ganin ana neman shafe minti guda ya katse shirun da faɗin, “Inada abinyi fa Malam”.

     Ƙaramar dariya akai daga can tare da faɗin, “Wannan girman kan naka da gizago kesani ƙara jin ka dace da buƙatar aikina Smart Mawashi. Mutanena sun sanar min ka koma aiki, weldone daka kasance mai biyayya irin haka da saurin gane abu....”

           “Na koma ne badan kurarinka ko farfagandarka ba! Ko a tunaninka sakawa ana bibiyata da kawomin wasu banzayen saƙwanni a takarda ko kiran wayata zaisa nayi abinda kake so?”.

    Ya faɗa cikin katseshi murya a dake. Dariya akayi da ga can, Alhaji ya ce, “Muɗauka haka ɗinne to. Sai dai ka sani ni samaniya ne mai rufe rufin kowanne gida da daji. Abinda kaga ya faru har ya kawoku asibiti yau ka ɗauka shine signing na contract ɗinmu da kai. Ya rage naka ka fara aiwatar da ayyukanka yanda ya dace ko kai kuskuren nunamin zafin kai na cigaba da nuna maka sauran kalolina. Dan a duk inda Jiƙamshi family suke ni nan da kake ji da gani zagaye nake da su har a cikin ɗakin kwanansu, har ma da kai kanka a yanzu....”

     Baki ya buɗe zai yi magana ƙittt aka yanke wayar, da sauri ya cirota daga kunnensa, ƙoƙarin kiran layin ya shigayi sai dai yaƙi shiga, ya koma wajen massage danya tura sai ya gama babu app na massage a wayar kwata-kwata. Cikin tsarguwa ya ɗan fara dube-dube, sai dai babu alamar wani da hankalinsa ke a kansa a eriya ɗin wajen gaba ɗaya. Wayarsa ya ciro ya kwashe number da zummar yin kira sai dai kuma taƙi shiga, wadda aka kirashi a farko ya gwada kira itama taƙi shiga. Yay ɗan shiru ransa a dagule, tunanin kiran wani abokinsa yay da zummar masa tracing layukan sai kuma ya fasa saboda tuna maganar mutumin. (A duk inda kake idanuna a kanka suke koda a cikin ɗakin barcinka ne). Fasawa yay ya maida wayar aljihu yana jin zuciyarsa ta masa nauyi da tunani kala daban-daban.  


        Gaba ɗaya wannan yinin haka ahalin Jiƙamshi gaba ɗaya suka yisa a asibitin tare da shi. Bai yi yinƙurin komai akan son sanin abinda ke damunta ba. Yana dai biye da motsin kowa har zuwa azhar da Uncle Yousuf ya buƙaci ya kaishi gida zai ɗan watsa ruwa. Sai da suka hau hanya yake tambayarsa ya mai jiki. Cikin damuwa Uncle Yousuf ya ɗan furzar da nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe kansa ya ce, “Da sauƙi za'ace, dan tunda muka zo sai yanzu ne aka samu kanta har barci ya ɗauketa. Shiyyasa nake son a yau mubar ƙasar nan dan ban taɓa ganin Muwaddat a cikin halin ciwo mai tsananin irin wannan ba. Ban san mi yarinyar ke son maida kanta ba, ban taɓa tunanin rashin jinta ya kai haka ba sai yau, yanzu doctor ya ɗan fara min bayanin wai shaye-shaye ne ke son jawo mata matsala, ban san wane irin rayuwa yarinyar nan take son kai kantaba kuma. Amma duk laifin Yaya ne da ke nuna mata ƙazamin gatan da shi a gurinshi yake ɗauka so ne...” yaja tsaki mai nuna tsananin ƙunar da zuciyarsa ke masa. Da gani kasan yana jin zafi ne a ransa har yake furta abinda bai kamata ya furta a gaban driver kamarsa ba. Sai dai shi kansa ya matuƙar girgiza dajin kalaman Uncle Yousuf ɗin. A ransa faɗi yake (No wander idanunta sam babu kunya da mutunci a cikinsu ashe ƴar shaye-shaye ce) wani irin tsanarta yaji ta sake ɗarsuwa a ransa, ashe bayan ballagazanci harda shaye-shaye. Da ƙyar ya iya furta ma Uncle Yousuf cewar “ALLAH dai ya bata lafiya Alhaji. Sai dai addu'a, a wannan zamanin yara mata da yawa suna cikin wannan mummunar ɗabi'ar ta shaye-shaye, wasu samari ke ɗorasu wasu ƙawaye, wasu matsin rayuwa maimakon suyi tawakkali da haƙuri su maida al'amarin su ga UBANGIJI sai su zaɓi wannan hanyar mara ɓillewa. Wasu ko tsabar gata ne da jin daɗin duniya ke kwasarsu. Sai dai fatan ALLAH ya shiryesu ya kare wanda kuma basu fara ba dan abin tashin hankalin harda matan aure ma yanzu”.

         Cikin tsananin damuwa Uncle Yousuf yace, “ALLAH ka shiryar mana da su. Kayi mana maganin duk wasu azzalumai dake safarar mugayen abubuwan nan zuwa ƙasashenmu suna ɓata mana yara”.

     “Amin ya rabbi”.

Ya amsa masa dai-dai yana shiga layin gidan Uncle Yousuf ɗin.....        ★A ranar bai samu damar zaman yin magana da Uncle Yousuf kan batun dawowarsa aiki ba. Dan yana shiga yay wanka sake fitowa yay suka koma asibitin. Zuwa yanzu kam ta samu barci kamar yanda yaji ƴan uwan na faɗama Uncle Yousuf. Sai a lokacin ya samu damar gaisawa da Daddy daya iso yanzu da ga Abuja da Mommy ya jajanta musu. Cikin ƙarfin hali Daddy ya ce, “Kamar yaron nan daka kawo ne kace kuma ya ajiye aiki jiya Yousuf?”.

       Kai tsaye Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Shine Yaya. Sai dai banyi magana da shi ba dai bayan wadda nace maka nayi, amma inaga ya dawo aikinsa ne”.

       Daddy ya ɗan ja numfashi da faɗin, “Dama Baby batace bata buƙatarsa ba ai. Amma mu jira har ALLAH ya bata lafiya sai muji ta bakinta dai”.

     “Uhum”

Kawai Uncle Yousuf yace. Mommy ma dai dake jinsu batace komai ba sai ma ɗauke kanta tai gefe dan haushin mijin nata akan ƴarsu da zata iya rantsuwa da ƙazamar soyayyar da yake matane duk ya zama silar komai na halin da take ciki a yanzu. Duk da dai basu ji komai da ga bayanin likita ba amma yanzu zasuje garesa suji ɗin. Su duka ukun suka nufi office ɗin Doctor Khalil Shira.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

No comments